Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Bukatun Musamman da Daidaiton Dama, Mohammed Abba Isa, ya bukaci ‘yan Najeriya, musamman al’ummar Musulmi, da su mara wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu baya yayin bikin Eid-el-Fitr.
A cikin wata sanarwa, Abba Isa ya taya Shugaba Tinubu, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, da daukacin Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.
Ya bayyana Ramadan a matsayin lokaci na sadaukarwa, ladabi, da sabunta rayuwar ruhaniya, inda ya bukaci Musulmi su ci gaba da rike dabi’un hakuri, tawali’u, karamci, da ibada ko bayan karewar watan azumi.
Haka kuma, Abba Isa ya jaddada muhimmancin hadin kai da zaman lafiya, yana mai kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da nuna kauna da tausayi ga juna, ba tare da la’akari da bambancin addini ba.
Ya kuma bukaci ‘yan kasa da su kasance masu kishin kasa tare da mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu baya domin cigaban kasa.
“A wannan lokaci mai muhimmanci a tafiyar kasarmu, dole ne ‘yan Najeriya su hada kai wajen gina kasa mai kyau inda babu wanda za a bari a baya,” in ji shi.
Ya bayyana fatan cewa bikin Eid zai kawo zaman lafiya, wadata, da sabon fata ga al’ummar Najeriya baki daya.
