Shugaban Cibiyar Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC), kuma shugaban Transparency International Nigeria, Auwal Musa Rafsanjani, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi darussan watan Ramadan domin inganta zaman lafiya, rikon amana, da kuma gina al’umma mai adalci da hadin kai.
Rafsanjani ya bayyana hakan ne cikin sakon taya murnar karshen azumin Ramadan da kuma bikin Eid-el-Fitr, inda ya ce watan Ramadan lokaci ne na sadaukarwa, horo, da kuma bunkasa ruhaniya.
Ya ce, “Yayin da muke bikin Eid, ya kamata mu ci gaba da rike darussan da muka koya a watan Ramadan, musamman wajen nuna tausayi, hakuri, da daukar nauyin al’umma baki daya.”
Ya kara da cewa akwai bukatar ‘yan kasa su hada kai domin gina kasa mai cike da adalci, wadda kowa zai samu dama ba tare da wariya ba.
Rafsanjani ya kuma yi fatan alheri ga Musulmai da daukacin ‘yan Najeriya, yana mai addu’ar samun zaman lafiya da farin ciki a lokacin bikin Eid.
Shi Rafsanjani shi ne Babban Daraktan CISLAC, shugaban Transparency International Nigeria, kuma yana rike da mukamai daban-daban ciki har da shugaban kungiyar Transition Monitoring Group da kuma shugabancin kwamitin amintattu na Amnesty International Nigeria.
