Hadaddiyar Kungiyar Masu Bukata ta Musamman ta Kasa (JONAPWD) ta kaddamar da wani shiri na kididdiga mai taken #AssumptiveDataOfPersonsWithDisabilities, inda ta bayyana cewa adadin masu bukata ta musamman a Najeriya ya kai kusan miliyan 35.
A cewar bayanan, Jihar Kano ce ke kan gaba da kimanin miliyan 2.5, sai Jihar Lagos da ke biye da miliyan 2.1.
Kididdigar ta kuma nuna cewa maza masu bukata ta musamman sun kai miliyan 17.6, yayin da mata suka kai miliyan 17.2.
Game da rabe-raben nau’o’i, masu larurar jiki ne suka fi yawa da kimanin miliyan 8.2, sai masu larurar ji da miliyan 7.7, da masu larurar gani da miliyan 7.2.
Sauran rukunan sun hada da masu fama da cutar kuturta, masu albinism, masu matsalar laka, da masu larurar kwakwalwa. Haka kuma, akwai wasu rukuni masu karanci amma masu muhimmanci kamar masu larurar ji da gani a lokaci guda da masu gajeren tsawo.
Kungiyar ta ce wadannan bayanai na nuni da cewa matsalar bukata ta musamman a Najeriya ta yadu sosai, tare da bukatar tsare-tsare na musamman da hadin gwiwa domin tabbatar da cikakken tallafi da shigar da su cikin al’umma.
